Sanarwa da kwamitin kolin sasanta rikicin Syria ya fitar, ta jaddada cewa ‘yan adawar za su aika wakilai 30 zuwa 35 birnin Geneva domin shiga tattaunawar amma ba da nufin cimma wata yarjejeniya ba.
Tuni dai kasashen Saudiya da Amurka suka yi marhaba da shawar da bangaren adawar ya yanke na shiga tattauawar kawo karshen yakin shekaru biyar a Syria.
A jiya jumma’a ne wakilan gwamnatin shugaba Bashar al Assad suka isa Geneva, inda suka yi ganawarsu ta farko da manzan musamman na majalisar dinkin duniya a Syria, Staffen de Mistura.288